Tankokin Iran uku sun kaucewa shingen da sojojin ruwan Amurka suka yi
Shafukan da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa sun bayar da rahoton cewa tankokin mai uku na Iran sun kaucewa shingen ruwan da rundunar sojan ruwan Amurka ta kafa, karo na farko cikin watanni biyu.
Binciken BBC Verify ya tabbatar da cewa tankokin, waɗanda ke ƙarƙashin takunkumi kuma mallakin Kamfanin Tankokin Mai na Iran, sun ketare layin shingen ɗauke da mai gabaɗaya, kafin su shiga Tekun Arabian Sea.
Rahoton ya ƙara da cewa duk da cewa na’urorin da ke nuna matsayin tankokin suna aiki, ba sa bayyana inda suke nufa, abin da ke nuna yadda ake ci gaba da safarar mai duk da tsauraran takunkuman da ake fuskanta.