Su wane ne gwanayen Alrqur'ani, kuma yaya ake samun matsayin?

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A tsawon ƙarnuka, al'adar koyon Alƙur'ani ta kasance ginshiƙin rayuwar Musulmi a Arewacin Najeriya da sauran sassan yankin Tafkin Chadi. Daga makarantu na allo zuwa manyan cibiyoyin ilimin addini, dubban ɗalibai kan sadaukar da rayuwarsu wajen haddacewa, rubutawa da kuma fahimtar Alƙur'ani mai girma.

Sai dai, a cikin wannan doguwar tafiya ta neman ilimi, akwai wani matsayi na musamman da ba kowa ne ke kaiwa gare shi ba.

Wannan matsayi shi ne na "Gwani", wata daraja da masana suka bayyana a matsayin ƙololuwar matsayi da ɗalibin Alƙur'ani zai iya kaiwa bayan shekaru masu yawa na karatu, jarrabawa da kuma nuna ƙwarewa. Tsawon lokaci, ana kallon mai wannan matsayi a matsayin jagora kuma abin koyi ga al'ummarsa, saboda zurfin iliminsa da kuma hidimar da yake yi wa Alƙur'ani.

Sai dai duk da yawan amfani da kalmar, mutane da dama ba su san haƙiƙanin tarihinta ba, ko yadda ake samun wannan matsayi, ko kuma irin sharuɗɗan da ake la'akari da su kafin a amince mutum ya zama gwani. Haka kuma, ana ci gaba da samun saɓanin ra'ayi kan wasu al'adun da ake dangantawa da gwanaye, ciki har da iƙirarin cewa suna iya karanta Alƙur'ani ta baya ko kuma ta baibai.

Masana da masu bincike sun ce matsayin gwani ba sabon abu ba ne a tarihin Musulunci a wannan yanki. Sun bayyana cewa ya samo asali ne tun daga Daular Kanem-Borno, inda aka gina tsari mai ƙarfi na horas da mahaddatan Alƙur'ani da tantance su kafin a amince su kai wannan matsayi.

Domin gano asalin wannan matsayi, tarihinsa, matakan da ake bi wajen samunsa da kuma matsayin da yake da shi a yau, mun tattauna da wasu masana da gwanayen Alƙur'ani daga Cibiyar Nazarin Alƙur'ani ta Jami'ar Bayero Kano da sauran fitattun malamai da suka shahara a wannan fanni.

Matsayin gwani

Farfesa Gwani Tijjani Zubairu Rabi'u na Cibiyar Nazarin Alƙur'ani ta Jami'ar Bayero Kano ya bayyana cewa kalmar Gwani wata kalma ce ta istilahi da ta samo asali daga al'adun Afirka, musamman Daular Kanem-Borno.

Ya ce: "Gwani ita ce daraja mafi girma da ɗalibin Alƙur'ani zai iya kaiwa bayan ya bi matakai daban-daban na karatu. A tsarin gargajiya, ita ce daraja ta takwas kafin a kai ga matsayin Sheikhul Qurra'i ko Muqri'u."

Dangane da asalin kalmar kuwa, Farfesan ya ce malamai sun yi mabambantan bayani.

"Wasu malamai sun danganta kalmar da ƙwarewa da fice a ilimi, wasu kuma sun ce tana da alaƙa da wadatuwa da ilimi da cikakken ƙwarewa a fagen Alƙur'ani."

Duk da canje-canjen da zamani ya kawo, masana sun yi ittifakin cewa matsayin Gwani na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan martabobi a al'adar karatun Alƙur'ani a yankin Kanem-Borno da ƙasar Hausa.

Sai dai kamar yadda suka bayyana, wannan matsayi ba suna ne kawai ba, illa wata shaida ce ta shekaru na jajircewa, bautar Allah da sadaukar da kai wajen hidimtar Alƙur'ani mai girma.

Matakan karatun Alƙur'ani

A cewar Farfesa Tijjani Zubairu Rabi'u, matakan da ɗalibi ke ratsawa kafin kaiwa matsayin gwani sun haɗa da:

  • Kolo
  • Kotso
  • Titibiri
  • Gardi
  • Alaramma
  • Mahiru
  • Gangaran
  • Gwani (wasu kuma su ce gangaran ne a gaban gwani)

Ya ƙara da cewa: "Bayan wannan akwai daraja ta tara, wato Sheikhul Qurra'i ko Muqri'i. Wannan matsayi ne da ya haɗa haddar Alƙur'ani, ilimin ƙira'o'i da sauran rassan ilimomin Alƙur'ani."

Daga ina kalmar Gwani ta samo asali?

Shi ma Gwani Bashir Mu'azzam ya danganta kalmar da asalin Larabci.

A cewarsa: "Gwani kalma ce da ta samo asali daga Larabci mai nufin wanda ya wadatu da Alƙur'ani. Mutanen Borno suka riƙa furta ta da 'Gooni', daga baya kuma Hausawa suka mayar da ita Gwani."

Masanan sun bayyana cewa saukan fari na nufin karanta Alƙur'ani gaba ɗaya daga farko zuwa ƙarshe ba tare da wani kuskure ba ta hanyar rubutawa ana karantawa a allo.

Gwani na farko a Najeriya

Masana sun ce Daular Borno ce ta fara tsarin naɗa gwanaye tun ƙarni na shida.

Farfesa Tijjani Zubairu Rabi'u ya ce: "Ba a naɗa gwani sai bayan cikakkiyar tantancewa. Ana tattara manyan malamai da gwanaye domin su tabbatar mutumin ya kai matsayin da ya iya Alƙur'ani ba tare da shakka ba."

Ya ƙara da cewa bikin naɗin gwani babban al'amari ne a zamanin da. "A wasu yankuna na Nijar da Chadi har yanzu idan aka naɗa mutum gwani, wannan suna ba ya rabuwa da shi har ƙarshen rayuwarsa. Hatta wasu unguwanni ana danganta su da sunan gwanin da ke cikinsu."

Dangane da wanda aka fara sani da wannan matsayi, ya ce: "Tarihin da Sheikh Sharif Salih ya kawo a littafinsa Al-I'tizak ya nuna cewa Gwani Musa bn Salih Al-Ajurumi, wanda aka fi sani da Gwani Musa Addanƙuli ne da aka fara naɗawa a matsayin gwani a Maiduguri, kuma ya yi karatu a Masar kafin ya koma Maiduguri ya zauna."

Siffofin Gwani

Masana sun jaddada cewa gwani ba kawai mahaddaci ba ne kamar sauran mahaddatan Alƙur'ani.

Shi ma Gwani Bashir Mu'azzam ya danganta kalmar da asalin Larabci.

A cewarsa: "Gwani kalma ce da ta samo asali daga Larabci mai nufin wanda ya wadatu da Alƙur'ani. Mutanen Borno suka riƙa furta ta da 'Gooni', daga baya kuma Hausawa suka mayar da ita Gwani."

Ya ce samuwar mutum a matsayin gwani a zamanin da ba abu ne mai sauƙi ba.

"Sai mutum ya haddace Alƙur'ani gaba ɗaya, ya iya rubutunsa, sannan ya yi abin da ake kira saukan fari ba tare da an gyara masa ko harafi ko wasali guda ba sau 41," in ji shi.

Farfesa Tijjani Zubairu ya ce an riƙa samun raguwa kan adadin saukan fari da ake buƙata har ya koma kusan 10.

Farfesa Tijjani Zubairu Rabi'u ya ce: "Abu na farko shi ne Alƙur'ani ya zama rayuwarsa. Hidimarsa ga Alƙur'ani ba ta yankewa, ko wajen karatu ko koyarwa ko nazari."

Shi kuwa Gwani Bashir Mu'azzam ya ce: "Gwani shi ne wanda babu shakka a karatunsa. Yana iya saukan fari cikin sauƙi kuma ya bambance ayoyin da suke kama da juna ba tare da kuskure ba."

Ya ƙara da cewa: "Za ka ga gwani yana karanta wata aya sannan yana rubuta wata aya makamanciyarta ba tare da ya rikice ba."

Aliyu Haruna Muhammad ya ce: "Gwanaye su ne mahaddatan Alƙur'ani da suka cika sharuɗɗan ƙwarewa da kyawawan ɗabi'u."

Ya lissafa daga cikin waɗannan siffofi:

  • Haddace Alƙur'ani gaba ɗaya.
  • Ingantaccen karatu ba tare da kura-kurai ba.
  • Yin saukan fari a gaban manyan malamai.
  • Kwarewa wajen rubuta Alƙur'ani.
  • Tsoron Allah da riƙon addini.
  • Cigaba da koyarwa da yaɗa ilimin Alƙur'ani.

Ya ce: "A baya ana buƙatar mutum ya yi saukan fari har sau talatin. Daga baya aka rage zuwa sau goma sha biyar, yanzu kuma a wasu wurare ana karɓar sau goma."

Karanta Alƙur'ani ta bai-bai

Wannan na daga cikin tambayoyin da ake yawan yi kamar yadda wasu ke yaɗawa cewa gwanaye na karanta Alƙur'ani ta baya.

A tattaunawarsa da BBC, Aliyu Haruna Muhammad daga Cibiyar Nazarin Alƙur'ani ya ce babu wani tushe da ke nuna cewa karanta Alƙur'ani ta baya sharaɗi ne na zama gwani.

Ya ce: "Babu inda aka ce gwani dole ne ya iya karanta Alƙur'ani ta baya. Allah ya saukar da Alƙur'ani cikin tsari, kuma haka aka umurce mu mu karanta shi."

Ya ci gaba da cewa: "Ba gwaninta ba ce mutum ya zo da abin da ya saɓa da yadda aka tsara Alƙur'ani. Wannan ba ya cikin sharuɗɗan zama gwani ko kaɗan."

Waye ke tantance Gwani?

Aliyu Haruna Muhammad ya bayyana cewa a tarihi babu wata hukuma ta musamman da aka ware domin tantance gwanaye.

A cewarsa: "Malamin da ɗalibi ya yi karatu a wajensa shi ne ya fi sanin matakin da ya kai. Idan ya ga ya cancanta, sai ya tuntuɓi sauran malamai da abokan karatunsa domin neman shawararsu."

Ya ƙara da cewa: "Idan malamai suka amince, to wannan amincewa ita ce tantancewar da take ba mutum damar shiga cikin gwanaye."

Masana sun ce samun cikakkiyar ƙididdigar gwanaye a yau abu ne mai wahala.

Farfesa Tijjani Zubairu Rabi'u ya ce: "A da idan za a naɗa gwani duk gari za a sani, kuma kusan duk gwanayen yankin za su halarta. Yanzu kuma ana samun naɗe-naɗe da yawa a wurare daban-daban, har a naɗa mutane da dama a lokaci guda."

Ya kuma yi nuni da cewa akwai waɗanda ake ba matsayin ne saboda hidimarsu ga Alƙur'ani da kishin da suke nuna wa littafin Allah.

"A wani ɓangare, matsayin gwani ya yi kama da matsayin digirin-digirgir a tsarin ilimin zamani."

Shi kuwa Gwani Rabi'u Ilyas daga Gwarzo a Jihar Kano ya ce: "Zai yi wahala a samu adadin gwanaye na gaskiya saboda akwai mutane da dama da suka kai wannan matsayi amma ba su yi fice ko shahara a cikin al'umma ba."