Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsaloli 5 da bashin da gwamnatin Najeriya ke karɓa zai yi wa ƙasar
Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton Bankin Duniya da ya nuna damuwa cewa biyan kuɗin ruwa na bashi ya kai tiriliyan N7.7 a farkon shekarar 2026 na iya zama barazana ga ɗorewar basussukan ƙasar.
A sabon rahotonsa na Nigeria Development Update (NDU), Bankin Duniya ya nuna damuwa kan yadda kuɗin da Najeriya ke kashewa wajen biyan basussuka ya zarce yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati a rabin farkon shekarar 2026, inda ya ƙiyasta adadin da kashi 124 cikin 100.
Ma'aikatar Kuɗi ta ce yanayin kuɗaɗen gwamnati ya inganta, kuma kuɗaɗen shiga na ƙaruwa cikin sauri fiye da yawan kuɗin ruwa da ake biya kan basussuka.
Cikin wata sanarwa da ministan kuɗin ƙasar Taiwo Ayodele ya wallafa a shafinsa na X ya ce rahoton na Bankin Duniya ba shi da inganci.
A cewar ma'aikatar kuɗin ƙasar, an yi wannan lissafi ne bisa wasu bayanan kuɗaɗen shiga da ba su cika ba, sannan an haɗa da bashin da Gwamnatin Tarayya ke biya a madadin gwamnatocin jihohi.
Haka kuma ta ce an bar wasu kuɗaɗen shiga da hukumomi da kamfanonin gwamnati suka samu amma har zuwa lokacin ba su kai ga baitul malin gwamnati ba.
Ma'aikatar ta kuma ƙara da cewa tsarin biyan wasu haraji a Najeriya na nufin cewa ana karɓar mafi yawan kuɗaɗensu ne a rabin ƙarshen shekara, don haka amfani da kuɗaɗen shiga na rabin farko kawai ba zai bayar da cikakken hoto wajen auna nauyin bashin shekara baki ɗaya ba.
"Ma'aikatar Kuɗin ta lura da wasu nazarce-nazarce da ra'ayoyin jama'a da suka dogara da rahoton Bankin Duniya na watan Oktoban 2026 kan ci gaban Najeriya, inda aka yi iƙirarin cewa kuɗin ruwa da Gwamnatin Tarayya ta biya a rabin farkon shekarar 2026 sun kai kashi 124 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta. Wannan batu da gaskiya ba ne''.
Dalilan gwamnatin Najeriya
Ma'aikatar kuɗin ta bayyana wasu dalilai guda uku da suka ce sun saboda dalilai uku, kamar haka:
A cewarta adadin kuɗin ruwa da aka lissafo ya haɗa da bashin da Gwamnatin Tarayya ke biya a madadin wasu matakan gwamnati, ciki har da bashin waje na jihohi.
''Saboda haka, kwatanta wannan da kuɗaɗen shigar Gwamnatin Tarayya kaɗai yana ƙara girman adadin fiye da yadda ya kamata, domin irin wannan ƙididdiga na da ma'ana ne kawai idan bashi da kuɗaɗen shiga suna magana ne kan matakin gwamnati guda ɗaya'', in ji sanarwar.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa adadin kuɗaɗen shiga da aka ruwaito bai cika ba, domin bai haɗa da wasu kuɗaɗen shiga masu zaman kansu da hukumomi da kamfanonin gwamnati suka riga suka samu amma ba su tura su baitul mali ba.
Haka kuma ma'aikatar kudin ta ce, a al'ada ana samun kuɗaɗen shiga masu yawa a rabin ƙarshen shekara fiye da rabin farkonta saboda lokacin da doka ta tanada na biyan wasu haraji.
''Wannan ne ya sa adadin ya kai kashi 156 cikin 100 a rabin farkon shekarar 2025, amma idan aka duba shekara baki ɗaya, kaso na biyan bashi idan aka kwatanta da kuɗaɗen shiga ya kasance ƙasa da kashi 60 cikin 100, sabanin kashi 97 cikin 100 kafin aiwatar da sauye-sauyen gwamnati'', in ji sanarwar.
Me masana tattalin arziki ke cewa?
Dr Murtala Abdullahi Ƙwara, malami a sashen nazarin tattalin arziki na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina ya ce abin da wannan ya nuna cea akwai matsala.
Malamin jami'ar ya ce abin da wannan ke nufi shi ne gwmanatin Najeriya ba ta fitar da ƙididdiga sahihiya game da tattalin arzikin ƙasar.
Dangane da ikirarin da gwamnatin Najeriya ta yi cewa Bankin Duniyar ya lissafa mata bashin ne tare da gwamnatocin jihohi da take karɓa, masanin tattalin arzikin ya ce ba haka batun yake ba.
''Ai shi bankin Duniya a ƙaramin banki ba ne da zai yi irin wannan kuskuren, banki ne da ke aiki da ƙwararrun masana da suka aikin banki'', in ji masanin tattalin arzikin.
Matsalolin da karɓar bashi zai yi wa Najeriya
Masanin tattalin arzikin ya lissafo wasu matsaloli da ya ce hakan zai jefa gwamnatin Najeriya da ma ƴan ƙasar, kamar haka:
- Rashin kuɗi
Dr Murtala Abdullahi Ƙwara ya ce ɗaya daga cikin matsalolin da hakan zai haifar shi ne rashin kuɗin gudanar da ayyuka da gwamnati za ta fuskanta.
''Wannan matsala na ma fara fuskantarta, don a alokuta da dama ana kokawa da hakan'', in ji shi.
- Ƙarin bashi
Wani abu da hakan zai janyo wa Najeriya shi ne ƙarin karɓo basuka daga ƙasashen waje.
''Idan ƙasa ta fuskanci rashin kuɗin gudanar da ayyuka, za ta koma domin karɓo ƙarin basuka, wanda kuma hakan zai ƙara dakula al'amura'', in ji shi.
- Gaza biyan bashi
Wata matsa da hakan zai janyo wa Najeriya shi ne gaza biyan basukan da ake binta a cewar masanin tattalin arzikin.
''Kuma hakan zai janyo matsaloli masu yawa, musammamn idan muka yi la'akariu da wasu ƙasashen da suka shiga irin wannan yanayi'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa idan hakan ta faru Najeriya za ta rasa kimarta a idanun duniya da cibiyoyin da ke bayar da basuka.
- Ƙarancin ayyukan more rayuwa
Malamin jami'ar ya ce idan aka ci gaba a haka gwamnatin Najeriya z ata rasa kuɗin gudanar da ayyukan more rayuwa ga talakawa.
''Fannonin lafiya da ilimi za su fuskanci koma-baya, waɗanda dama yanzu ma ya ake ciki?'', in ji shi.
- Matsin tattalin arziki
A cewar masanin tattalin arzikin hakan zai jefa Najeriya cikin karin matsin tattalin arzikin.
''Idan kuwa aka samu kai a wannan yanayi rayuwa za ta kara tsananta, talaka zai shiga mawuyacin hali'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Me ya kamata gwamnatin ta yi?
Masanin tattalin arzikin ya ce abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta ti shi ne rasge kashe kuɗaɗe bai gaira ba dalili mai alaƙa da cin hanci da rashawa.
''In kuma ta kama sai an ciwo bashi, to ya kamata a samo bashi domin yin abin da yake da muhimmanci da zai amfani ci gaban ƙasar'', kamar yadda ya bayyana.
Sannan kuma ya ce yana da kyau gwamnati ta samar da wasu hanyoyi na samun kuɗaɗen shiga domin rage dogaro da bashin.
''Haka kuma yana d akyau gwamnati ta riƙa bayyana gaskiya na alƙaluman da take fitarwa dangane da tattalin arzikin ƙasar'', in ji shi.